Hukumar Kula da Rajistar Hayar Kayan Aiki (ELRA) da Asusun Bunƙasa Aikin Noma na Kasa (NADF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa da nufin saukaka wa manoma samun injinan noma ta hanyar tsarin haya.
Jami’an bangarorin biyu sun bayyana cewa shirin zai taimaka wajen samar da taraktoci, injinan girbi, na ban ruwa da sauran kayan aikin noma ga manoma da masu harkokin noma a fadin kasar nan. Sun ce wannan mataki zai rage matsalar karancin kayan aikin noma, kara yawan amfanin gona da kuma taimakawa wajen tabbatar da wadatar abinci a Najeriya.
Haka kuma, an bayyana cewa yarjejeniyar za ta karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, cibiyoyin kudi da kamfanonin samar da kayan aikin noma domin bunkasa harkar noma da inganta tattalin arzikin kasa.
