Jam’iyyar Democratic Leadership Alliance (DLA) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 da ta fito da ingantattun matakan da za su dakile matsalar garkuwa da mutane da ke kara kamari a fadin kasar nan. Jam’iyyar ta bayyana cewa ‘yan Najeriya na rayuwa cikin tsoro yayin da masu aikata laifuka ke ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da tsangwama ba.
DLA ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mataimakiyar sakatariyar yada labaranta ta kasa, Judith Aguenu, ta sanya wa hannu, inda ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ayyana matsalar garkuwa da mutane a matsayin ta-baci ta kasa tare da daukar matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Jam’iyyar ta kuma yi gargadin cewa idan ba a samu ci gaba mai ma’ana cikin kwanaki 14 ba, za ta bi hanyoyin dimokuradiyya da na shari’a domin jan hankalin gwamnati da masu ruwa da tsaki kan halin da ‘yan Najeriya ke ciki sakamakon matsalar rashin tsaro.
