Kungiyar Daliban Najeriya (NANS) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta sanya wakilan dalibai cikin kwamitin gaggawa da aka kafa domin dakile yaduwar cutar Ebola a kasar nan.
Bukatar na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Obidah David, ya fitar a madadin shugabancin NANS.
Kungiyar ta yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kafa kwamitin yaki da Ebola, tana mai bayyana matakin a matsayin wani muhimmin shiri na kare lafiyar ‘yan Najeriya.
Shugaban NANS, Akinteye Babatunde, ya ce kasancewar wakilan dalibai a cikin kwamitin zai taimaka wajen yada sahihan bayanai da fadakarwa a jami’o’i, kwalejojin ilimi da polytechnics a fadin kasar nan.
Ya bayyana cewa dalibai na daga cikin manyan rukunin jama’ar da ke bukatar wayar da kai kan hanyoyin kariya daga cututtuka masu yaduwa, musamman saboda rayuwar da suke yi tare a dakunan kwanan dalibai da wuraren karatu.
NANS ta kuma bayyana shirinta na hada kai da hukumomin lafiya da cibiyoyin ilimi wajen gudanar da gangamin fadakarwa kan hanyoyin kariya, gano alamun cutar da kuma bin ka’idojin lafiya.
Kungiyar ta ce sanya wakilan dalibai cikin kwamitin zai kara tabbatar da gaskiya, rikon amana da kuma isar da bayanan lafiya ga dalibai a sassan kasar nan.
Ta kuma bukaci gwamnatin tarayya ta yi la’akari da wannan bukata domin karfafa yaki da duk wata barazanar barkewar cutar Ebola a Najeriya.