Hukumar Tara Haraji ta Jihar Taraba (Taraba State Internal Revenue Service) ta gargadi mazauna jihar da masu kasuwanci da su guji biyan haraji cikin asusun banki na kashin kai, tana mai jaddada cewa dukkan biyan haraji dole ne ya kasance ta hanyoyin gwamnati da aka amince da su.
Shugaban hukumar, Birgediya Janar Jeremiah Faransa (mai ritaya), ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Jalingo yayin wani gangamin wayar da kai a fadin jihar kan sabbin sauye-sauyen dokokin haraji.
Gangamin ya hada kungiyoyin ‘yan kasuwa, mata ‘yan kasuwa, bankuna da sauran masu ruwa da tsaki, da nufin ilmantar da jama’a kan sabbin dokokin haraji tare da karfafa bin doka cikin yardar rai.
Faransa ya ce manufar shirin ita ce karfafa amincewar jama’a ga tsarin tara kudaden shiga na jihar da kuma tabbatar da fahimtar sauye-sauyen haraji da ake aiwatarwa.
Ya gargadi cewa babu wani mutum da aka ba izinin karbar haraji a madadin gwamnati ta hanyar asusun kashin kai.
A cewarsa, duk wanda aka kama yana karbar haraji ba bisa ka’ida ba ko karkatar da kudaden gwamnati zai fuskanci hukunci mai tsauri daga doka.
Ya kuma bukaci jama’a da su rungumi sauye-sauyen, yana mai cewa biyan haraji yana da matukar muhimmanci wajen ci gaban jihar da samar da ayyukan more rayuwa.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana shirin a matsayin mai amfani kuma wanda ya dace da lokaci, suna masu cewa zai taimaka wajen dakile almundahanar haraji da inganta bin doka a tsakanin ‘yan kasa.
