Gwamnatin Jihar Kwara ta yi kira ga mata masu juna biyu da su rika yin rajista da wuri domin kula da lafiyarsu a lokacin daukar ciki tare da halartar dukkan lokutan duba lafiyar da aka tsara musu a asibiti.
Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Lafiya ta jihar, Dakta Taoheed Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kan jama’a da aka shirya domin inganta lafiyar mata masu juna biyu da jarirai.
Ya ce yin rajista da wuri da kuma halartar dukkan lokutan duba lafiya na taimakawa wajen sa ido kan lafiyar uwa da jariri tare da gano matsaloli cikin lokaci domin daukar matakan da suka dace.
A cewarsa, ya kamata mata masu juna biyu su tabbatar sun haihu a cibiyoyin lafiya karkashin kulawar kwararrun ma’aikatan jinya domin tabbatar da tsaron rayuwar uwa da jariri.
Abdullahi ya kara da cewa gano matsalolin da ke tattare da daukar ciki da wuri da kuma magance su cikin lokaci na daga cikin manyan hanyoyin rage mace-macen mata masu juna biyu da na jarirai.
Ya kuma bayyana cewa an raba kayan haihuwa ga mata masu juna biyu a lokacin taron domin karfafa musu gwiwa wajen zuwa asibiti, haihuwa a cibiyoyin lafiya da kuma shirye-shiryen haihuwa cikin aminci.
A nata bangaren, jami’ar kula da ayyukan Asusun Majalisar Dinkin Duniya Kan Yawan Jama’a (UNFPA), Gloria Enueze, ta bayyana cewa ungozomomi na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da lafiyar uwa da jariri tun daga lokacin daukar ciki har zuwa bayan haihuwa.
Ta kuma jaddada muhimmancin tsarin tsara iyali, tana mai cewa tazarar haihuwa mai kyau na rage hadurran lafiya ga uwa da yara tare da taimakawa wajen gina iyalai masu koshin lafiya.
Tun da farko, shugabar sashen lafiya ta karamar hukumar Ilorin East, Hajiya Sulyman Ajibola, ta bukaci mata masu juna biyu su yi amfani da kayan haihuwar da aka ba su tare da kwanciya cikin gidan sauro mai magani domin kariya daga cutar zazzabin cizon sauro da sauran cututtukan da sauro ke yadawa.
Masu shirya taron sun bayyana cewa shirin wani bangare ne na bikin Ranar Ungozoma ta Duniya, wadda ake gudanarwa a ranar 5 ga watan Mayu na kowace shekara domin yabawa irin gudunmawar da ungozomomi ke bayarwa wajen kare lafiyar iyaye mata da jarirai.
