Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Sagbama/Ekeremor ta Jihar Bayelsa, Hon. Fred Agbedi, ya zama sabon Jagoran ‘Yan Adawa (Minority Leader) a Majalisar Wakilai ta Tarayya.
Agbedi, wanda mamba ne na bangaren PDP karkashin jagorancin Taminu Turaki, ya gaji Hon. Kingsley Chinda wanda ya yi murabus daga mukamin tare da sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki bayan samun nasara a zaben fidda gwani na gwamnan jihar Rivers.
Haka kuma, dan majalisar mai wakiltar Darazo/Ganjuwa ta Jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), Hon. Manu Soro, ya zama Minority Whip, yayin da Hon. Abdulsamad Dasuki na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) daga Jihar Sokoto ya zama Mataimakin Jagoran ‘Yan Adawa.
An sanar da sabbin nade-naden ne ta wata wasika daga ‘yan adawa a majalisar da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya karanta a zaman majalisa na ranar Alhamis.
Wasikar ta bayyana cewa an cimma matsaya guda kan zabin sabbin shugabannin ba tare da hamayya ba.
Nadin ya kawo karshen rikicin shugabanci da ya dauki makwanni ana yi tsakanin ‘yan adawa, bayan sama da ‘yan majalisa 60 daga cikin 80 suka nuna goyon baya ga Hon. Ikenga Ugochinyere domin ya zama Jagoran ‘Yan Adawa.
Sai dai kafin hakan, Majalisar Wakilai ta yi gyara ga dokokinta inda ta haramta wa sababbin ‘yan majalisa masu wa’adi na farko rike manyan mukaman shugabanci a majalisar.
Sabon gyaran dokar ya tanadi cewa dole ne dan majalisa ya kammala akalla wa’adi guda na shekaru hudu a majalisar kafin ya cancanci rike mukamin shugaban masu rinjaye ko ‘yan adawa.
Bayan sauyin dokar, Ugochinyere ya janye takararsa ta neman zama Jagoran ‘Yan Adawa, yana mai bayyana cewa ya dauki matakin ne domin mutunta sabbin dokokin majalisar da kuma kare martabar majalisar.
Masu sharhi kan siyasa na ganin sabuwar tawagar shugabannin ‘yan adawa za ta taka muhimmiyar rawa wajen hada kan jam’iyyun adawa daban-daban da kuma karfafa sa ido kan ayyukan gwamnati a gabanin babban zaben shekarar 2027.
