Kamfanin TikTok ya bayyana cewa ya cire sama da bidiyo miliyan 4 a Najeriya tare da dakatar da fiye da zaman kai tsaye (LIVE) 86,000 a zangon karshe na shekarar 2025, a wani mataki na karfafa tsaro da ingancin amfani da dandalin.
A cikin rahoton sa na Q4 2025 kan aiwatar da dokokin amfani (Community Guidelines Enforcement Report), kamfanin ya ce an cire jimillar bidiyo miliyan 4.02 da suka karya dokokin dandali a Najeriya.
Rahoton ya bayyana cewa kashi 99.9 cikin 100 na wadannan bidiyo an gano su ne ta hanyar tsarin atomatik kafin masu amfani su kai rahoto, yayin da kashi 98.4 cikin 100 aka cire su cikin sa’o’i 24 bayan wallafawa.
TikTok ya ce wadannan alkaluma na nuna yadda kamfanin ke kara amfani da fasahar gano abun da bai dace ba domin kare masu amfani da rage yaduwar abun cutarwa.
A matakin duniya kuwa, TikTok ya ce ya cire sama da bidiyo miliyan 175.3 a wannan lokaci, wanda ke wakiltar kusan kashi 0.5 cikin 100 na dukkan abun da ake wallafawa a dandali.
Kamfanin ya kuma ce sama da bidiyo miliyan 152.5 an cire su ta hanyar tsarin atomatik, yayin da aka dawo da wasu bidiyo miliyan 8.4 bayan sake dubawa.
A bangaren LIVE, TikTok ya ce ya dakatar da fiye da zaman kai tsaye 86,000 a Najeriya saboda karya dokokin amfani da dandali.
A duniya baki daya, an dauki mataki kan sama da zaman LIVE miliyan 17.7 da kuma masu kirkirar abun ciki miliyan 9.2 da suka karya dokokin monetisation.
Kamfanin ya kuma ce yana kara yaki da abun da aka kirkira da fasahar AI, inda yake tilasta wa masu amfani su sanya alama idan abun AI ne, tare da amfani da fasahar gano irin wadannan abubuwa.
Rahoton ya ce an gano sama da bidiyo biliyan 1.3 na AI a duniya an sanya musu alama domin nuna asalinsu.
TikTok ya jaddada cewa yana hada fasahar zamani da kwararrun masu sa ido domin tabbatar da tsaron dandalin.
A karshe, kamfanin ya ce zai ci gaba da hadin gwiwa da hukumomin gwamnati da kungiyoyin farar hula, ciki har da Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, domin inganta tsaro a yanar gizo da yaki da abun da zai iya cutar da jama’a.
