Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana cewa jam’iyyar APC na cikin fargaba sakamakon yadda jam’iyyar Accord ke kara samun karbuwa a fadin jihar.
Adeleke ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da masu yakin neman zabe 10,000 da dan takarar kujerar Majalisar Wakilai na mazabar Ijesa North karkashin Accord, Hon. Pelumi Olajengbesi, ya shirya a garin Ijebu-Jesa.
Gwamnan ya ce dumbin jama’ar da suka halarci taron ya nuna cewa Accord na kara karfi a jihar duk da sauya shekar wasu ‘yan majalisa zuwa wasu jam’iyyu.
Ya ce APC ta rasa farin jini a wajen al’ummar Osun, yayin da jama’a ke ci gaba da nuna goyon baya ga gwamnatinsa da kuma jam’iyyar Accord.
Adeleke ya yaba wa al’ummar Ijesa bisa ci gaba da mara masa baya, tare da yabawa Pelumi Olajengbesi saboda yadda ya hada kan magoya bayan jam’iyyar a yankin.
Ya bayyana Olajengbesi a matsayin mutum mai jajircewa wanda zai iya kayar da manyan ‘yan adawa a zabe mai zuwa.
A nasa bangaren, Olajengbesi ya ce an shirya taron ne domin kaddamar da masu yakin neman zabe 10,000 tare da nuna cikakken goyon bayan al’ummar Ijesa ga sake zaben Gwamna Adeleke.
Ya kara da cewa mutanen mazabar Ijesa North sun yi imanin cewa nasararsa da kuma sake zaben Adeleke ne kadai za su kawo ci gaba da ‘yantar da yankin daga matsalolin da suke fuskanta.
Shi ma shugaban PDP na Jihar Osun, Sunday Bisi, ya bayyana cewa kuri’un da Adeleke zai samu daga yankin Ijesaland a zabe mai zuwa za su fi wadanda zai samu daga garin Ede, mahaifarsa.
Kalaman sun zo ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zabukan shekarar 2027.
