Kungiyar Hadin Kan Jam’iyyun Siyasa ta Kasa (IPAC) reshen Jihar Cross River ta bukaci jam’iyyun siyasa a fadin Najeriya da su rungumi gaskiya, adalci da zaman lafiya yayin da ake shirin gudanar da babban zaben shekarar 2027.
Kiran na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban IPAC na jihar, Injiniya Effiom Edet Okon, tare da sakataren yada labarai na kungiyar, James Otudor, suka fitar bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Calabar domin bikin Ranar Dimokuradiyya ta 2026.
Kungiyar ta ce zaman lafiya da kwanciyar hankalin siyasa da ake samu a jihar Cross River ya samo asali ne daga kyakkyawar alaka da fahimtar juna tsakanin jam’iyyun siyasa.
A cewar IPAC, dimokuradiyya ba za ta bunkasa ba sai an tabbatar da adalci, gaskiya da kuma bai wa kowa damar shiga harkokin siyasa ba tare da nuna bambanci ba.
Kungiyar ta bukaci ‘yan siyasa da su mayar da hankali wajen karfafa cibiyoyin dimokuradiyya domin kara gina amincewar jama’a gabanin sabon zagayen zabuka.
Ta kuma yi kira da a samar da yanayin siyasa mai cike da fahimtar juna, mutunta doka da bin ka’idojin dimokuradiyya domin kauce wa duk wani rikici da zai iya tayar da zaune tsaye.
IPAC ta jaddada cewa samar da ayyukan ci gaba da amfanar jama’a shi ne hanya mafi kyau ta samun goyon bayan al’umma da kuma tabbatar da dorewar dimokuradiyya.
Kungiyar ta kara da cewa tattaunawa tsakanin jam’iyyu, warware sabani cikin lumana da kuma bai wa matasa da mata dama a harkokin siyasa na daga cikin muhimman hanyoyin tabbatar da shugabanci nagari.
A karshe, IPAC ta sake tabbatar da kudirinta na ci gaba da inganta zaman lafiya, hadin kai da karfafa dimokuradiyya a Najeriya yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2027.
