Shugabar Ƙungiyar Manoma ta Ƙaramar Hukumar Ojo a Jihar Legas, Mrs. Mayriam Ali, ta yi gargaɗin cewa farashin kayan lambu da ganyayyaki zai ƙaru a makonni masu zuwa sakamakon ambaliyar ruwa da ta lalata gonaki a Ojo da wasu sassan jihar.
Ta bayyana cewa mamakon ruwan sama ya nutsar da gonaki, ya lalata amfanin gona tare da hana manoma girbi da sake shuka amfanin gona.
A cewarta, kayan lambu irin su ugu, alayyahu (spinach), spring onion, oregano da waterleaf na daga cikin waɗanda za su fi fuskantar tashin farashi.
Mrs. Ali ta ce kunshin waterleaf da ake sayarwa kan kimanin Naira 500 na iya haura zuwa tsakanin Naira 1,000 da Naira 1,300 saboda asarar da manoma suka yi.
Ta yi kira ga gwamnati da ta samar wa manoma injinan famfo masu amfani da hasken rana, tare da inganta hanyoyin sufuri domin rage asarar amfanin gona da ƙarfafa samar da abinci.
