Uwargidan Gwamnan Jihar Anambra, Dr. Nonye Soludo, ta bayyana farin cikinta bayan cikakkiyar warkewar yaro ɗan shekara 10 mai suna Chiziterem, wanda aka ce masu kula da shi sun yi masa mummunar azabtarwa.
Yaron ya shafe makonni yana karɓar magani a ƙarƙashin kulawar gwamnatin jihar bayan wani bidiyo da ya nuna raunuka da ƙone-ƙone a jikinsa ya bazu a kafafen sada zumunta, lamarin da ya jawo hankalin jama’a.
Dr. Nonye Soludo, wadda ta ɗauki nauyin kula da yaron tun bayan faruwar lamarin, ta ce zuciyarta ta cika da godiya ganin cewa Chiziterem ya warke gaba ɗaya kuma an sallame shi daga asibiti.
Ta gode wa duk waɗanda suka yi masa addu’a, suka ziyarce shi, suka ba da gudummawa ko suka nuna tausayi, tana mai cewa goyon bayansu ya taka muhimmiyar rawa wajen samun lafiyarsa.
Uwargidan gwamnan ta kuma bayyana cewa ta biya duk kuɗaɗen jinyar yaron, tare da alƙawarin tallafa wa mahaifiyarsa da jarin sana’a domin ta samu damar kula da ‘ya’yanta cikin walwala.
- A watan Yunin 2026 ne jami’an ‘yan sandan Jihar Anambra suka kama wata mata mai suna Chisom Chukwukere da mijinta Chukwudi, bisa zargin azabtar da yaron ta hanyar ƙona jikinsa da robobi masu zafi, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar.
