Hukumar Tara Harajin Cikin Gida ta Jihar Delta (DSIRS) ta sake jaddada cewa haramcin kafa shingayen hanya da karɓar haraji a gefen tituna na nan daram a faɗin jihar, tare da gargadin cewa duk wanda aka kama yana aikata hakan za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
Shugaban Hukumar DSIRS, Hon. Solomon Ighrakpata, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya nuna damuwa kan yadda wasu mutane da ƙungiyoyi ke ci gaba da kafa shingayen hanya ba bisa ka’ida ba suna karɓar kuɗaɗen haraji da sunan hukumomin gwamnati.
Ya ce irin waɗannan ayyuka suna kawo cikas ga tsarin karɓar haraji na doka tare da jefa direbobi da ‘yan kasuwa cikin wahala.
A cewarsa, babu wani mutum, ƙungiya ko hukuma da ke da izinin tare ababen hawa ko karɓar haraji a kan tituna, domin duk biyan kuɗaɗen gwamnati ya kamata a yi shi ne ta hanyoyin biyan kuɗi na zamani da gwamnati ta amince da su.
Ighrakpata ya bayyana cewa wasu ƙungiyoyi, ƙungiyoyin kwadago da ma wasu jami’an ƙananan hukumomi, a wasu lokuta tare da haɗin gwiwar wasu jami’an ‘yan sanda marasa gaskiya, suna kafa shingayen hanya tare da tilasta wa direbobi biyan kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba.
Ya jaddada cewa dokokin ƙasa, ciki har da Dokar Gudanar da Haraji ta Najeriya ta 2025 da kuma Dokar Haraji da Kuɗaɗen Shiga da Aka Amince da Su, sun haramta karɓar haraji a kan hanyoyin jama’a.
Shugaban DSIRS ya kuma bayyana cewa hukumar ba ta nada wani wakili ko kamfani domin karɓar harajin hanya ko kuɗaɗen jigilar kaya na shekarar 2026.
“Duk wanda yake ikirarin wakiltar DSIRS wajen karɓar haraji a kan hanya yana aikata zamba ne, kuma ya kamata a kama shi tare da hukunta shi bisa doka,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa duk wani tsarin haɗin gwiwa da masu ba da shawara kan karɓar haraji yana dakace har sai an amince da sabuwar Dokar Harajin Jihar Delta ta 2026.
Hukumar ta kuma yi kira ga jama’a, direbobin sufuri da shugabannin ƙananan hukumomi da su guji mu’amala da duk wanda ke ikirarin wakiltar DSIRS ba tare da sahalewar hukuma ba.
Haka kuma, ta buƙaci jami’an tsaro, musamman Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, da su kamo tare da gurfanar da duk masu kafa shingayen hanya ko wuraren karɓar kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba.
DSIRS ta ce za ta ci gaba da tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kare yanayin kasuwanci a jihar daga duk wani tsangwama na haramtattun masu karɓar haraji.
