Wani mai gudanar da harkar ruwa, Alhaji Adetona Mubashiru, ya yi kira ga Hukumar Kwastam ta Najeriya Nigeria Customs Service da ta sake duba dokar gwamnatin tarayya da ta hana shigo da motocin ta kan iyakokin kasa, yana mai cewa matakin ya kara haifar da fasa-kwauri tare da rage kudaden shiga na gwamnati.
Mubashiru, wanda shi ne shugaban kamfanin Only God is Wise Nigeria Limited, ya ce dokar da aka fara aiwatarwa a 2017 ta gaza cimma manufarta, inda ta tura harkar shigo da motoci zuwa hanyoyin haram da dazuka a iyakoki marasa tsaro.
Dokar da aka sanar a ranar 5 ga Disamba, 2016 a karkashin tsohon shugaban Kwastam, Col. Hameed Ali (rtd), ta fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2017, inda ta hana shigo da sabbin motoci da na amfani ta kan iyakokin kasa, bisa umarnin gwamnatin tarayya.
Ya ce maimakon rage fasa-kwauri, dokar ta kara yawaitar amfani da hanyoyin da ba su dace ba, wanda ya sa jami’an Kwastam ke fuskantar matsaloli wajen shawo kan harkar.
A cewarsa, hakan ya kuma haifar da asarar kudaden shiga ga gwamnati, yayin da ‘yan kasuwa ke karkatar da kayayyaki zuwa kasashen makwabta musamman Jamhuriyar Benin.
Mubashiru ya ce kafin a kafa dokar, akwai yarjejeniya tsakanin Najeriya da Benin kan shigo da motoci ta tashar Cotonou, inda Kwastam ke raka su zuwa Seme domin tantance su yadda ya dace.
Ya kuma ce matsalar rashin wurin ajiye motoci da aka taba fuskanta a baya a kan iyaka yanzu an magance ta, domin wuraren Seme na iya daukar motoci sama da 1,000 a lokaci guda.
Ya kara da cewa sake bude iyakokin zai taimaka wajen farfado da tattalin arziki tare da samar da ayyukan yi ga matasa da masu sana’o’i kamar makanikai, masu gyaran mota da direbobi.
A karshe ya bukaci a sake tattaunawa kan manufar bisa ka’idojin cinikayya na duniya, tare da yabawa shugaban Kwastam na yanzu, Adewale Adeniyi, kan kokarinsa na tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
