Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta yi kakkausar suka kan sace dalibai, malamai da jami’an makarantu yayin hare-haren da aka kai makarantu a yankunan Ahoro-Esinele da Yawota da ke karamar hukumar Oriire a jihar Oyo.
Kungiyar ta bayyana lamarin a matsayin abin kunya ga kasa baki daya, tare da gargadin cewa wannan na nuna yadda matsalar tsaro da ayyukan ta’addanci ke kara bazuwa zuwa yankin Kudu maso Yamma.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Archbishop Daniel Okoh, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, CAN ta nuna matukar fusata kan yadda ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka mamaye makarantu da dama da rana tsaka, suka firgita al’umma, suka kashe mutane marasa laifi tare da yin garkuwa da dalibai da malamai da dama.
Kungiyar ta ce kai hari makarantu, wadanda ya kamata su kasance wuraren ilimi da kariya, na nuna mummunan tabarbarewar tsaro a kasar nan.
CAN ta bukaci gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa domin ceto wadanda aka sace tare da tabbatar da tsaron makarantu a fadin kasar.
Kungiyar ta kuma jaddada cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba da zama kasa inda yara ke shiga makaranta cikin fargaba ba, tana mai kira ga daukar matakan gaggawa domin dakile wannan matsala.
