Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta kama mutane shida da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a kusa da Jami’ar Bayero Kano (BUK) Old Site.
An gudanar da samamen ne a ƙarƙashin shirin “Operation Sharar Mafaka”, bayan korafin da hukumar gudanarwar jami’ar ta gabatar kan yawaitar ayyukan saye da shan miyagun ƙwayoyi a wasu sassan harabar jami’ar da kewayenta.
Kakakin hukumar, Sadiq Maigatari, ya ce an rushe wasu wuraren da ake zargin ana gudanar da haramtacciyar kasuwanci tare da ƙwace tare da lalata kayan da aka samu a wurin.
Ya bayyana cewa Kwamandan NDLEA na Jihar Kano, CN DY Lawal, ya ce wannan mataki na nuna jajircewar hukumar wajen tabbatar da muhalli mai tsabta daga miyagun ƙwayoyi musamman a cibiyoyin ilimi.
“Wannan aiki yana nuna ƙudurinmu na tabbatar da yanayi mai tsabta daga miyagun ƙwayoyi inda ɗalibai da ma’aikata za su zauna cikin kwanciyar hankali,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen fatattakar masu aikata laifuka da rushe wuraren da ake safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.
Hukumar ta yaba da haɗin gwiwar jami’ar Bayero Kano, tana mai cewa rahoton da aka kai ya taimaka wajen gudanar da samamen cikin gaggawa da nasara.
NDLEA ta kuma gargadi jama’a da ke amfani da cibiyoyin gwamnati wajen harkokin miyagun ƙwayoyi da su daina, tana mai cewa za a hukunta duk wanda aka kama.
Haka kuma ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano da kuma kawar da wuraren da ake aikata irin waɗannan laifuka a Jihar Kano.
