Fitaccen jigo a jam’iyyar Nigerian Democratic Congress (NDC), Buba Galadima, ya bukaci tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, da ya shiga jam’iyyar domin hada kan ‘yan adawa gabanin babban zaben 2027.
Galadima ya yi wannan kira ne a ranar Litinin yayin wata tattaunawa a shirin Politics Today na Channels Television, inda ya ce manyan ‘yan siyasar adawa na hada kai a karkashin NDC domin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.
Ya ce akwai bukatar hadin kan ‘yan adawa domin samun nasara a zaben 2027, yana mai gargadin cewa rashin shiga Atiku cikin wannan tafiya na iya zama masa nauyi a siyasa.
“Gaskiyar magana ita ce Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sun shiga ADC, sun zo da manufar hada kan ‘yan adawa domin cire gwamnatin Tinubu,” in ji Galadima.
Ya kara da cewa akwai zarge-zargen cewa gwamnatin APC na amfani da kotuna wajen raunana jam’iyyun adawa, lamarin da ya ce ya kara bukatar hadin kai.
“Ina kiran tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da ya biyo mu kamar yadda muka biyo shi zuwa ADC, domin a samu cikakken hadin kan ‘yan adawa,” in ji shi.
Galadima ya kara da cewa idan Atiku ya ki shiga wannan tafiya, zai iya zama abin da za a dora masa alhakin rashin nasarar hadin kan ‘yan adawa a 2027.
Kiran nasa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa da hadakar jam’iyyun adawa a fadin Najeriya gabanin zaben mai zuwa.
