Tsohon ɗan wasan Najeriya, Osaze Odemwingie, ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga Victor Osimhen, inda ya ce kada ya kuskura ya koma Manchester United, yana mai cewa kulob ɗin na iya lalata makomar ‘yan wasan gaba.
Odemwingie ya yi wannan bayani ne a wata hira da Brila FM, inda ya bayyana cewa Manchester United na matuƙar matsin lamba ga ‘yan wasan gaba saboda girman kulob ɗin da kuma buƙatar samun nasara nan take.
“Na ga matsalar Manchester United tana da girma sosai. Matsin lamba kan ‘yan wasan gaba yana da yawa. Ya kamata a guje musu,” in ji shi.
Ya ce tarihin kulob ɗin ya nuna yadda manyan ‘yan wasan gaba suka kasa biyan buƙatu saboda matsin lamba, yana kawo misali da Romelu Lukaku da wasu da dama.
Odemwingie ya kuma ba Osimhen shawarar cewa ya fi dacewa ya zaɓi manyan kulob-kulob da suka fi kwanciyar hankali kamar:
Arsenal
Barcelona
Real Madrid
Ya ce waɗannan kulob-kulob sun fi dacewa da haɓaka ƙwarewar ɗan wasan maimakon su murƙushe shi da matsin lamba.
“Arsenal da Barcelona za su dace da Osimhen. Real Madrid ma kulob ne mai kyau a gare shi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa salon wasan Osimhen—ƙarfi, gudu da iya kai ƙwallo sama—zai fi dacewa a Real Madrid saboda faɗin fili da tsarin wasan su.
A halin yanzu, Osimhen yana taka rawar gani a Galatasaray, inda ya zura kwallaye 13 a gasar lig da kuma 7 a Champions League, tare da taimakon kwallaye biyar.
Duk da rashin nasara da suka yi kwanan nan, ya tabbatar zai ci gaba da fafutuka domin lashe kofin gasar Turkiyya kafin ya yanke shawarar makomar sa.
