Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa har yanzu bai tantance cikakken sabon tayin zaman lafiya da Iran ta gabatar ba, amma ya nuna cewa akwai yiwuwar ba zai amince da shi ba.
Trump ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce Iran ba ta “biya isasshen farashi ba” kan abubuwan da ya zarge ta da aikatawa tsawon shekaru da dama.
“Ba zan iya tunanin amincewa da wannan tayin ba, domin har yanzu Iran ba ta fuskanci isasshen hukunci ba,” in ji Trump.
Wannan furuci na zuwa ne yayin da Trump ke ci gaba da aika saƙonni masu rikitarwa game da yiwuwar sake kaddamar da hare-haren sama kan Iran, duk da cewa ya bayyana burinsa na kawo ƙarshen rikicin da aka shafe sama da watanni biyu ana yi.
A gefe guda, rikicin ya kara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya bayan Isra’ila ta umarci dubban mazauna kudancin Lebanon da su bar garuruwansu sakamakon hare-haren da take kaiwa kan kungiyar Hezbollah.
Iran ta bayyana cewa ba za ta ci gaba da tattaunawa da Amurka ba sai idan tsagaita wuta ta tabbata a Lebanon.
Sabon shirin zaman lafiya da Iran ta gabatar reportedly ya kunshi:
Bude hanyoyin jiragen ruwa a mashigin Hormuz
Kawo karshen takunkumin Amurka
Sakin kadarorin Iran da aka daskarar
Janye dakarun Amurka daga yankunan da ke kewaye da Iran
Tattaunawa kan shirin nukiliya a gaba
Sai dai Amurka ta dage cewa dole ne Iran ta fara mika tarin uranium mai yawa da take da shi kafin a cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
Rikicin ya janyo babbar tangarda ga samar da makamashi a duniya, musamman bayan toshewar mashigin Hormuz wanda ke dauke da kusan kashi 20 cikin 100 na safarar mai da iskar gas na duniya.
Masana na gargadin cewa rikicin na iya kara jefa tattalin arzikin duniya cikin matsin lamba, yayin da farashin mai da makamashi ke ci gaba da hauhawa.(
Add A Comment
