Ƙungiyar Birnin-Gwari Vanguard for Security and Good Governance ta yaba wa Gwamnatin Tarayya da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa tabbatar da amincewar aikin hanyar Naira biliyan 178, tana mai cewa hakan na nuna cika alkawuran da aka yi wa al’umma kafin zaɓen 2023.
Ƙungiyar ta kuma nuna godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa cika alkawuran da ya yi wa mutanen yankin Birnin-Gwari a lokacin yaƙin neman zaɓe.
A cikin sanarwar da shugabanta Ibrahim Nagwari ya fitar, ƙungiyar ta ce:
“Muna nuna godiya mai zurfi ga Gwamna Uba Sani bisa tabbatar da amincewar Gwamnatin Tarayya kan aikin hanyar Naira biliyan 178. Wannan mataki ya zama wani muhimmin sauyi ga al’ummarmu da suka sha fama da rashin tsaro da rashin ababen more rayuwa.”
Ƙungiyar ta kuma ce ta tuna da ziyarar da Shugaban Ƙasa ya kai Birnin-Gwari kafin zaɓen 2023, inda ya yi alkawarin magance matsalolin yankin, tana mai cewa ana ganin sakamakon wannan alkawari a yanzu.
Ta bayyana aikin hanyar Mando–Birnin-Gwari a matsayin mai muhimmanci ta fuskar al’umma da tsaro, tana cewa zai inganta haɗin kai, ƙarfafa aikin tsaro, da kuma bunƙasa noma da tattalin arziƙi.
“Wannan hanya za ta inganta haɗin kai, ƙarfafa tsaro, sauƙaƙa harkokin noma, tare da dawo da kwarin gwiwa ga al’ummomin da suka daɗe cikin keɓewa,” in ji ƙungiyar.
Ƙungiyar ta kuma yaba wa gwamnatin Kaduna kan wasu ayyukan ci gaba da take aiwatarwa, ciki har da gina hanyar Bagoma–Gagumi mai tsawon kilomita 36 da kuma kafa kasuwar shanu ta zamani da mahauta a Birnin-Gwari
A bangaren tsaro kuma, ƙungiyar ta ce shirin samar da zaman lafiya na gwamnatin jihar ya fara haifar da sakamako, musamman ta hanyar sauƙin zirga-zirga a hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna cikin watanni 18 da suka gabata.
Ta kuma ce harkokin noma sun fara farfadowa, inda manoma ke komawa gonakinsu yayin da damina ke gabatowa.
Duk da yabon da ta yi, ƙungiyar ta bukaci gwamnatin jihar da ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya ta hanyar ƙarfafa tattaunawa da al’umma domin sulhu da ci gaba.
Birnin-Gwari dai, wanda ke haɗa Kaduna da wasu sassan Arewa maso Yamma da Kudancin Najeriya, ya dade yana fama da matsalar ‘yan bindiga da hare-hare, lamarin da ya taɓa durƙusar da harkokin tattalin arziƙi da tilasta wa jama’a ƙaura.
Sai dai tun bayan hawan Uba Sani a shekarar 2023, gwamnati ta ƙara zage damtse wajen amfani da hanyoyin sulhu da kuma tsaro domin dawo da zaman lafiya, wanda ke fara haifar da sauƙi a yankin.
