- Tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Labour Party kuma jigo a African Democratic Congress (ADC), Peter Obi, ya bayyana matukar damuwarsa kan ikirarin shugaban Hukumar EFCC cewa shida cikin daliban jami’o’in Najeriya goma na da hannu a damfara ta intanet, yana mai cewa wannan batu babbar alama ce ta lalacewar tarbiyya da tsarin kasa baki daya.
- A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Obi ya ce idan har wannan ikirari gaskiya ne, Najeriya na fuskantar babbar matsala wadda ta wuce batun aikata laifi kawai, tana nuna rugujewar kyawawan dabi’u da tsarin rayuwar al’umma.
Obi ya bayyana cewa adadin daliban manyan makarantu a Najeriya bai wuce miliyan biyu zuwa miliyan 2.5 ba, yana mai cewa idan kashi 60 cikin 100 daga cikinsu suna shiga damfara, hakan na nufin kusan matasa miliyan 1.4 na cikin mummunar hanya.
“Acewar sa Idan har wannan gaskiya ne, to ba wai matsalar laifi kawai muke fuskanta ba, muna fuskantar rugujewar tarbiyya da tsarin kasa.”
Obi ya jaddada cewa dabi’un matasa yawanci suna fitowa ne daga irin tsarin da suke gani a cikin al’umma, musamman idan suna ganin masu laifi ko marasa gaskiya na cin moriyar rayuwa ba tare da hukunci ba.
Ya ce idan masu rike da manyan mukamai suna fuskantar zarge-zargen rashin gaskiya ko takardun bogi ba tare da fuskantar hukunci ba, hakan na aika sakon cewa mutum zai iya cin nasara ta kowace hanya.
