Wata kotu a jihar Nevada, Amurka, ta yanke wa tsohon ɗan wasan fim, Nathan Chasing Horse, hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da laifin cin zarafin mata da ‘yan mata ‘yan asalin ƙasar (Indigenous women and girls).
Chasing Horse, wanda ya fito a fim ɗin Dances With Wolves, ya bayyana a kotu ranar Litinin sanye da kayan gidan yari yayin da aka karanta hukuncin. Alkali Jessica Peterson ce ta yanke hukuncin bayan wata kotun jurors ta same shi da laifin wasu tuhume-tuhume 13 da suka shafi fyade da cin zarafi.
An zarge shi da cin zarafin mata uku, ciki har da wata da ta ce lamarin ya fara ne tun tana da shekara 14. Duk da haka, an wanke shi daga wasu tuhume-tuhume.
Wadanda abin ya shafa da iyalansu sun bayyana cewa har yanzu suna fama da mummunan rauni na tunani da abin ya haifar musu, inda suka ce ya yi amfani da matsayin da yake da shi a matsayin jagoran ruhaniya wajen yaudararsu.
A lokacin karanta hukuncin, Chasing Horse ya musanta laifin yana mai cewa: “Wannan rashin adalci ne.”
Masu gabatar da kara sun ce ya yi amfani da kimarsa a matsayin “lakota medicine man” wajen yaudarar mata da ‘yan mata tsawon kusan shekaru 20.
Daya daga cikin wadanda abin ya shafa ta bayyana yadda aka yi amfani da addini da ruhi wajen matsa mata lamba har ta fuskanci cin zarafi.
Hukuncin ya kawo karshen shari’ar da ta dauki shekaru ana kokarin gurfanar da shi, bayan kama shi a shekarar 2023.
Rahotanni sun kuma nuna cewa akwai wasu tuhume-tuhume da ke jiran shi a wasu yankunan Kanada, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike kan lamarin.
Wadanda abin ya shafa sun ce duk da wahalar da suka sha, suna fatan wannan hukunci zai zama sabon mafari na warkewa da neman adalci.
