Farashin kaji da ƙwai na ci gaba da ƙaruwa a fadin Najeriya sakamakon ƙarancin abinci ga kaji da kuma wahalar samun jarin aiki, lamarin da ke shafar masu kiwon kaji a ƙasar.
Masana harkar kiwon kaji sun ce tsadar abincin kaji da ƙarancin matasa kaji (young birds/pullets) na rage yawan samarwa, abin da ke barazana ga wadatar abinci da lafiyar al’umma.
A cewarsu, wannan matsala na haifar da ƙarancin kaji da ƙwai a kasuwa, wanda ke janyo tashin farashi ga masu saye.
A martani, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana shirin kawo matakan da za su daidaita farashin kaji da kuma ƙara yawan samarwa a fannin.
Ministan Harkokin Kiwo, Idi Mukhtar Maiha, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin ganawa da Ƙungiyar Masu Kiwo Kaji ta Najeriya (PAN).
Ya ce gwamnati za ta mayar da hankali kan rage manyan abubuwan da ke ƙara tsadar kiwo, musamman abincin kaji, makamashi da sauran kayan aiki.
Maiha ya kuma ce gwamnati na bukatar ingantaccen bayanai daga masu ruwa da tsaki domin tsara manufofi masu amfani, inda ya bukaci ƙungiyar ta samar da cikakken jerin hatcheries na ƙasa baki ɗaya.
“Za mu aiwatar da manufofin da za su rage tsadar kiwo ba tare da rage inganci ba,” in ji shi.
Shugaban PAN, Sunday Ezeobiora, ya ce fannin na fuskantar matsaloli da dama ciki har da tsadar abinci, ƙarancin kajin kiwo, cututtuka da kuma rashin samun rancen kuɗi.
Ya yi gargadin cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba, matsalar na iya ci gaba da rage wadatar kaji a kasuwa da kuma ƙara tsada.
Gwamnatin ta kuma ce tana duba hanyoyin rage tsadar kayan kiwo da inganta hanyoyin rarrabawa, tare da ƙarfafa saka jari a bangaren sarrafawa, ajiyar kaya da sufuri.
