Jos, Plateau State – Babbar Kotun Jihar Plateau ta bayar da umarnin tsare wasu mutane huɗu da ake zargi da hannu a kisan gillar da ya faru a Angwan Rukuba, karamar hukumar Jos North, har zuwa ranar 30 ga Afrilu, 2026.
Alkalin kotun, Justice Gidelia Damulak Fomyong, ya yanke wannan hukunci a ranar Alhamis bayan da aka kasa fara shari’ar (arraignment) sakamakon rashin lauyan kare wadanda ake zargin.
An tsare wadanda ake zargin ne a hannun Department of State Services (DSS), domin sauƙaƙa ci gaba da bincike kan lamarin.
Wadanda ake tuhuma sun hada da Isa Umar Ibrahim, Auwalu Abubakar (wanda aka fi sani da Auwalu Dogo), Musa Abubakar Ibrahim (Yaroro), da wani mutum guda. Hukumar DSS ta cafke su ne tsakanin 3 zuwa 10 ga Afrilu, 2026.
Zarge-Zargen Da Ake Fuskanta
Gwamnatin Jihar Plateau ta shigar da tuhume-tuhume a kansu da suka hada da haɗa baki wajen aikata ta’addanci da kuma tallafawa harin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 30.
Takardar karar, wadda Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Philemon Daffi ya sanya wa hannu, ta ce wadanda ake zargin sun tsara, suka shirya, tare da bayar da gudummawar kudi domin kai harin.
An ce laifukan sun saba da sashe na 269 kuma hukuncinsu na karkashin sashe na 270 na dokar Penal Code ta Jihar Plateau ta 2017.
Abin Da Ya Faru A Kotu
A zaman kotun, wadanda ake zargin sun roƙi a ba su lokaci domin su samo lauyoyin da za su kare su. Lauyan gwamnati kuma Solicitor-General na jihar, Joel Tagven, bai yi adawa da bukatar ba, amma ya nemi a ci gaba da tsare su a hannun DSS.
Kotun ta amince da bukatar kuma ta dage shari’ar zuwa ranar 30 ga Afrilu domin fara gabatar da tuhume-tuhumen a hukumance.
Martanin Iyalan Wadanda Ake Zargi
A wani bangare, ‘yan uwa da abokan hulɗar wasu daga cikin wadanda ake zargin sun musanta zargin da ake musu, suna mai cewa su ‘yan kasuwa ne kawai da ba su da hannu a lamarin.
Sun bukaci hukumomi da su tabbatar da an yi adalci, tare da jaddada cewa babu wanda aka kama da makami ko wata hujja da ke danganta su da harin.
Bayanin Gwamnati Da Shugaban Ƙasa
Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya taba bayyana harin a matsayin kisan kiyashi, yana mai cewa dole ne a kawo ƙarshen tashin hankalin a jihar.
Shi ma Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya tabbatar da cewa za a yi adalci ga waɗanda abin ya shafa, tare da kira ga al’umma da su kasance cikin shiri da lura.
Harin da ya faru a ranar 28 ga Maris, 2026, ya shafi yankunan Bokkos da Bassa, ciki har da Angwan Rukuba, inda sama da mutane 30 suka rasa rayukansu, ciki har da yara.
Ana sa ran fara shari’ar a ranar 30 ga Afrilu, yayin da bincike ke ci gaba da gudana.
