Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta bayyana cewa ta buɗe ƙofofinta ga ’yan jam’iyyun siyasa daban-daban a faɗin ƙasar nan, tare da nuna ƙwarin gwiwar cewa za ta lashe zaɓen 2027.
Da yake zantawa da manema labarai a Owerri, babban birnin Jihar Imo, a ranar Alhamis, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na ƙasa mai kula da shiyyar Kudu maso Gabas, Chief Teddy Obey, ya bayyana NDC a matsayin “tsabtatacciyar jam’iyya mara tabo” ga ’yan Najeriya da suka gaji da “alkawuran da ake maimaitawa.”
A cewarsa,
“Najeriya na neman tsabtatacciyar jam’iyya mara tabo. Wannan jam’iyya ita ce NDC.”
Obey ya jaddada cewa babbar ƙarfinsu ita ce kasancewar su sabuwar jam’iyya a Najeriya wadda ba ta da rikice-rikicen cikin gida ko shari’o’in kotu da suka addabi wasu jam’iyyu.
“Ku je ku bincika. Sauran jam’iyyu na kotu suna takaddama kan shugabanci. Mu kuma muna fili muna gina tsari. Gida mai rabuwar kai ba zai tsaya ba. Amma gida marar shari’a zai tsaya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa zuwansa Jihar Imo domin gudanar da wani taro ne a wuri mai zaman kansa domin ƙarfafa haɗin kai da gaskiya a cikin jam’iyyar.
“Na farko, domin magance koke-koke a fili. Na biyu kuma, domin kauce wa duk wani zargi na son kai. NDC sabuwar jam’iyya ce, dole mu nuna wa ’yan Najeriya cewa mun bambanta,” in ji shi.
A wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa jam’iyyar a jihar, Obey ya sanar da sabbin naɗe-naɗen wucin gadi. An naɗa Reginald Uwakwe a matsayin Shugaban Jam’iyyar na wucin gadi a Jihar Imo, yayin da Fabian Onyekwulisi zai jagoranci kwamitin tuntuba da wayar da kai da kuma na tantance ’yan takara.
Jam’iyyar NDC ta ce za ta ci gaba da faɗaɗa tushenta a matakin ƙasa yayin da take shirin zama madadin da za a dogara da shi a zaɓen 2027.
