Wasu tsofaffin ‘yan sanda a Najeriya, ƙarƙashin ƙungiyar Police Retired Officers Forum of Nigeria, sun tare ƙofar shiga Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin, suna gudanar da zanga-zanga kan tsarin fansho na Contributory Pension Scheme (CPS).
Tsofaffin jami’an tsaro sun ce suna bukatar a cire ‘yan sanda daga tsarin CPS, wanda suka bayyana a matsayin “marar adalci, ba bisa doka ba, kuma yana cutar da rayuwarsu”.
Masu zanga-zangar sun rika rike kwalaye da rubuce-rubuce kamar “End CPS” da “Me ya sa soja da DSS suka fita amma ‘yan sanda suka rage?”, yayin da suke rera kiraye-kirayen neman a sauya tsarin.
Sun ce manufar su ita ce su roki Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya rattaba hannu kan dokar da Majalisar Ƙasa ta amince da ita a ranar 4 ga Disamba, 2025, wadda ta shafi fitar da ‘yan sanda daga tsarin CPS.
Wani tsohon ASP, Nurudeen Dahiru, ya bayyana cewa sun shafe shekaru 35 suna aiki amma yanzu suna cikin matsanancin halin rayuwa
Ya ce: “Ba mu zo neman fada ba, mun zo neman hakkinmu ne. Mun wahala sosai. Yanzu ba mu iya kula da iyalanmu ba, ba mu da abin da za mu ci. Wannan tsarin fansho yana kashe mu a hankali.”
Shi ma wani tsohon jami’i ya ce albashin da ake biyansu bayan ritaya ya yi ƙasa sosai, inda ya koka da cewa ba ya wadatar da su.
Shugaban ƙungiyar, CSP Raphael Irowainu (mai ritaya), ya ce sun je Fadar Shugaban Ƙasa ne domin roƙon a amince da dokar fitar da ‘yan sanda daga CPS, wadda Majalisar Tarayya ta amince da ita.
Ya ce sauran hukumomin tsaro kamar soja, DSS, Navy, Air Force da NIA an cire su daga tsarin, amma ‘yan sanda sun rage a ciki.
Zanga-zangar ta zo ne bayan jerin irin wannan matsin lamba da tsofaffin ‘yan sanda ke yi a baya, ciki har da zanga-zangar da suka yi a Majalisar Ƙasa da kuma hedikwatar ‘yan sanda a Abuja.
