Tsohuwar Ministar Ilimi, Oby Ezekwesili, ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su ƙara ɗaukar nauyi wajen tabbatar da ingantaccen shugabanci da gyaran tsarin zaɓe a ƙasar.
A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na sada zumunta a ranar Laraba, Ezekwesili ta soki matakin shugabanci a manyan cibiyoyin gwamnati, ciki har da Majalisar Dokoki ta Ƙasa da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta (INEC).
Ta ce akwai ƙarancin kishin aiki ga jama’a a tsakanin wasu ‘yan siyasa, tana mai cewa hakan na hana samun ci gaba mai ma’ana a ƙasar.
A cewarta, ba za a iya samun gyaran gwamnati ba sai idan ‘yan ƙasa sun tashi tsaye wajen neman shugabanni nagari da rikon amana.
Ezekwesili ta kuma nuna damuwa kan sahihancin tsarin zaɓe a Najeriya, tana tambayar yadda wasu manyan malamai ke shiga cikin harkokin INEC idan ba za su yi aiki da gaskiya ba.
Ta kuma bayyana cewa ta taɓa kalubalantar shugaban INEC a wani taron tattaunawa a Abuja, inda ta ce ba su da cikakken imani da alƙawuran da hukumar ke bayarwa kan zaɓe mai inganci.
Tsohuwar ministar ta ƙara jaddada cewa idan ‘yan Najeriya ba su tashi tsaye ba, matsalolin rashin shugabanci nagari za su ci gaba da ƙara ta’azzara.
