Hukumomin ƙasar Iran sun kashe akalla mutane 1,639 a shekarar 2025, a cewar wani rahoto na kungiyoyin kare hakkin bil’adama guda biyu.
Rahoton, wanda ƙungiyoyin Iran Human Rights (IHR) da Together Against the Death Penalty (ECPM) suka fitar, ya nuna cewa wannan adadi ya karu da kusan kashi 68 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar 2024.
Kungiyoyin sun bayyana cewa adadin ya haɗa da mata 48, kuma suna ganin wannan shi ne mafi yawa tun bayan da aka fara tattara irin wadannan bayanai a shekarar 2008.
Rahoton ya kuma yi gargadin cewa idan gwamnatin Iran ta ci gaba da kasancewa a wannan yanayi na rikici, akwai yiwuwar amfani da hukuncin kisa zai ƙaru a matsayin hanyar murkushe jama’a.
Daraktan ECPM, Raphael Chenuil-Hazan, ya bukaci kasashen yamma da su sanya batun dakatar da hukuncin kisa a gaba yayin duk wata tattaunawa da Iran.
A gefe guda, daraktan IHR, Mahmood Amiry-Moghaddam, ya nuna damuwa cewa tattaunawar da aka yi tsakanin Amurka da Iran ba ta mayar da hankali kan hakkin jama’ar Iran ba.
Rahoton ya kuma nuna cewa daruruwan masu zanga-zanga da aka kama suna cikin hadarin fuskantar hukuncin kisa, musamman bayan zanga-zangar da aka yi a watan Janairu 2026.
