Fitacciyar ‘yar kafar sada zumunta, Blessing Okoro Nkiruka wacce aka fi sani da Blessing CEO, na fuskantar ƙorafi a gaban Economic and Financial Crimes Commission bisa zargin damfara, kirkirarren rahoton lafiya da kuma cin zarafin mutane a intanet.
A cewar takardar ƙorafi da aka shigar ranar 8 ga Afrilu, 2026, iyalan wata mata mai suna Mbara Deborah sun zargi Blessing CEO da sauya bayanan lafiyarta domin yaudarar ‘yan Najeriya tare da karɓar sama da naira miliyan 300.
An shigar da ƙorafin ne ta hannun lauyoyi S.M. Anyanwu & Co (Chieze Chambers), inda aka ce Blessing CEO ta yi amfani da shahararta a kafafen sada zumunta wajen tara kuɗaɗe da sunan taimakawa Deborah, amma bisa zargin bayanan da aka karkatar.
Rahoton ya nuna cewa Deborah, ‘yar kasuwa a fannin kwalliya da ke zaune a Asaba, an gano tana da cutar kansar mama (breast cancer) a shekarar 2025 a wani asibiti mai suna Xinus Medical Diagnostic.
Sai dai ana zargin Blessing CEO ta canza rahoton lafiyar zuwa matakin ƙarshe (Stage 4 cancer) domin jawo tausayi daga jama’a, wanda hakan ya taimaka wajen tara makudan kuɗaɗe.
Takardar ƙorafin ta ce, “An yi amfani da rahoton da aka canza domin damfarar ‘yan Najeriya masu tausayi da suka bayar da sama da naira miliyan 300 domin wata cutar da ba ta kai wannan matakin ba.”
Iyalan Deborah sun kuma zargi influencer ɗin da cin zarafi a intanet (cyberbullying) bayan sun yi ƙoƙarin fallasa gaskiyar lamarin.
An nuna cewa takardar ƙorafin ta samu karɓuwa a ofishin shugaban EFCC da ke Abuja a ranar 8 ga Afrilu, 2026.
Iyalan na neman a gaggauta kama tare da gurfanar da Blessing CEO a gaban kotu, suna mai cewa wannan lamari ya nuna rashin tausayi da amfani da wahalar wani domin anfani na kai.
Idan binciken Economic and Financial Crimes Commission ya tabbatar da zargin, akwai yiwuwar ta fuskanci tuhume-tuhume da suka haɗa da damfara, kirkira (forgery) da kuma cin zarafin yanar gizo.
