Babban mai kula da sashen cututtukan da ba sa yaduwa (NCDs) a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Dr. Alayo Sopekan, ya bayyana cewa kashi 8 cikin 100 na ‘yan Nigeria na rayuwa da ciwon suga, yayin da kashi 14 ke fama da hawan jini, sannan kusan kashi 25 na dauke da kwayar cutar sikila.
Sopekan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron horaswa kan yadda za a samar da kudade da aiwatar da tsare-tsaren yaki da cututtukan NCD, wanda aka gudanar a Mararaba, jihar Nasarawa State.
Taron ya samu hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da kungiyoyi irin su Legislative Initiative for Sustainable Development da kuma Global Health Advocacy Incubator.
A cewarsa, alkaluman sun fito ne daga wani bincike na baya-bayan nan (STEP survey) kan yawan da yadda cututtukan NCD ke karuwa, inda ya gargadi cewa mutane da dama ba su san halin da lafiyarsu ke ciki ba saboda rashin yin gwajin lafiya akai-akai.
Ya ce, “Ƙoƙarin da Najeriya ke yi wajen yaki da cututtukan da ba sa yaduwa na fuskantar ƙalubale saboda ƙarancin kuɗaɗe da kuma ƙarancin tallafin abokan hulɗa, duk da cewa irin wadannan cututtuka na ƙaruwa idan aka kwatanta da masu yaduwa da ke samun kulawa sosai.”
Sopekan ya jaddada muhimmancin gano cututtuka da wuri, rigakafi, da kuma kula da marasa lafiya domin rage illa da kuma dakile yaduwar matsalolin.
Ya kuma bukaci a ƙara ware kuɗaɗe daga harajin kayan giya, taba sigari, da abubuwan sha masu zaki domin tallafawa yaki da cututtukan NCD.
A nasa bangaren, Muntasir Liman ya bayyana cewa cututtukan da ba sa yaduwa na da alhakin kusan kashi 30 cikin 100 na mace-mace a Najeriya a kowace shekara, bisa ga sakamakon wani bincike na ƙasa da aka gudanar a 2023 wanda ya shafi sama da mutane 24,000.
