Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ekiti ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a satar babura tare da karɓar baburan sata, inda ta kuma kwato babura bakwai da ake kyautata zaton an sace.
Mai magana da yawun rundunar, SP Sunday Abutu, ya ce an kama Mustapha Lekan mai shekaru 38 daga Jihar Osun bisa zargin satar babura, yayin da aka kama Blessing Adebiyi da Ogunbayo Adebiyi bisa zargin karɓar baburan sata.
Abutu ya bayyana cewa jami’an sashen yaki da manyan laifuka sun samu bayanan sirri cewa an sace wata jajayen babur kirar Bajaj a yankin Ado-Ekiti, inda suka bi sawun wanda ake zargin har suka kama shi tare da kwato baburin.
A binciken farko, Mustapha ya amsa cewa ya sace babura biyu a Ado-Ekiti. Wannan ya kai jami’an tsaro zuwa Ilogbo Ekiti da Ido Ekiti, inda aka kama sauran mutane biyun tare da ƙwato ƙarin babura shida.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano masu ainihin baburan da aka kwato tare da kamo sauran waɗanda ke cikin wannan ƙungiyar ta masu aikata laifi.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ekiti, Michael Falade, ya yabawa jami’an bisa gaggawar da suka nuna wajen gudanar da aikin, tare da jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka a faɗin jihar.
