Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Najeriya (NIPR) ta yi gargaɗi kan ƙaruwa da masu aikin hulɗa da jama’a (Public Relations – PR) da ba su da lasisi, tana mai cewa hakan na lalata martabar sana’ar tare da yaudarar hukumomi da kamfanoni.
Shugaban NIPR na Jihar Rivers, Rev. Francis Asuk, ya bayyana hakan yayin bikin Ranar Hulɗa da Jama’a ta Duniya ta 2026 da aka gudanar a Jami’ar Ignatius Ajuru da ke Fatakwal.
Ya ce duk wanda ba mamba ba ne mai rijista a NIPR ba shi da izinin gudanar da aikin PR, tare da kira ga masu sha’awar shiga sana’ar su yi rijista domin samun horo da lasisin aiki.
Asuk ya bayyana cewa aikin PR ya wuce yaɗa labarai kawai, inda ya zama muhimmin fanni na tsara dabarun sadarwa, gina amincewar jama’a da kare mutuncin hukumomi da kamfanoni.
A nasa jawabin, Farfesa Kenneth Nweke ya ce a wannan zamani na fasahar sadarwa, PR ya zama ginshiƙi wajen gina amana, tabbatar da gaskiya da inganta shugabanci.
Shi ma Shugaban NIPR na ƙasa, Dr. Ike Neliaku, ya ce masu aikin PR a yau sun zama masu tsara manyan dabarun shugabanci da kare martabar cibiyoyi, yana mai kira gare su da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da riƙon amana.
