Gwamnatin Jihar Yobe ta amince da kashe Naira miliyan 460.83 domin ƙarfafa mata masu ƙananan sana’o’i, ciki har da masu sana’ar kosai, a faɗin jihar.
An amince da wannan shiri ne a taron Majalisar Zartarwa ta Jiha da Gwamna Mai Mala Buni ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Damaturu.
Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Yaɗa Labarai da Al’adu, Abdullahi Bego, ya ce shirin na da nufin inganta rayuwar mata masu ƙananan sana’o’i ta hanyar samar musu da kayan aikin da za su bunƙasa kasuwancinsu.
A cewarsa, gwamnatin ta amince da sayen buhuna 1,780 na wake mai nauyin kilo 50 domin rabawa mata masu sana’o’i, tare da man girki, murhun girki mara hayaƙi, tukwane da sauran kayan girki da tuni ma’aikatar samar da arziki da ƙarfafa tattalin arziki ta tanada.
Bego ya kuma bayyana cewa Majalisar ta amince da kashe Naira miliyan 364.48 domin sayen injinan niƙa Yamaha GX 390 guda 1,000, waɗanda za a raba wa al’umma a matsayin tallafin bunƙasa sana’o’i.
Haka kuma, ya ce gwamnatin ta amince da aiwatar da ayyuka da hidimomi da darajarsu ta kai Naira biliyan 73.32 a fannoni daban-daban na tattalin arzikin jihar.
Waɗannan sun haɗa da:
Naira biliyan 28.53 domin sayen kayan aikin noma a shirin bunƙasa noma na shekarar 2026.
Naira biliyan 23.97 domin manyan ayyukan gina hanyoyi guda biyu.
Kuɗaɗe domin ayyukan gidaje, kasuwanni da sauran muhimman ayyukan more rayuwa.
Gwamnatin Yobe ta ce waɗannan shirye-shiryen na daga cikin matakan inganta tattalin arziki, rage talauci da ƙarfafa mata da matasa a faɗin jihar.
