yajin aikin sai baba-ta-gani da ya fara, bayan sake nazarin halin tsaro a jihar.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Shugaban NUT na jihar, Hassan Fatai, da Sakataren kungiyar, Olukayode Salami, suka sanyawa hannu ranar Laraba.
Kungiyar ta ce ta dauki matakin dakatar da yajin aikin ne bayan tattaunawa da rokon da gwamnatin jihar Oyo da sauran masu ruwa da tsaki suka yi.
Sanarwar ta kara da cewa kungiyar ta yi la’akari da ingantuwar yanayin tsaro kafin yanke shawarar komawa bakin aiki, wanda hakan zai bai wa malamai damar komawa azuzuwa domin ci gaba da koyar da dalibai.
A baya dai malaman sun shiga yajin aikin ne sakamakon damuwarsu kan sace wasu daliban makaranta da aka yi a yankin Ogbomosho, karamar hukumar Orire, inda suka bukaci gwamnati ta kara inganta matakan tsaro a makarantu a fadin jihar Oyo.
