Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta sanar da fara daukar sabbin ma’aikata na shekarar 2026, tare da bayyana sharudda 15 da duk mai neman aiki dole ne ya cika kafin ya gabatar da bukatarsa.
Hukumar ta ce za a bude shafin neman aikin ta intanet daga Jumma’a, 3 ga Yuli, 2026, kuma za a ci gaba da karbar aikace-aikace na tsawon makonni hudu.
FRSC ta jaddada cewa daukar aikin kyauta ne, tare da gargadin jama’a da kada su biya kowa kudi da sunan samar musu da aiki.
Muhimman sharuddan neman aikin sun hada da:
Dole ne mai nema ya kasance dan Najeriya ta haihuwa.
Ya cika shekarun da aka tanada ga mukamin da yake nema.
Ya kasance mai ilimin amfani da kwamfuta.
Ya kasance cikin koshin lafiya ta fuskar jiki da kwakwalwa.
Ya kasance bai yi aure ba.
Maza su kasance a kalla tsayin mita 1.65, mata kuma mita 1.58.
Masu neman mukaman kwararru kamar likitoci, ma’aikatan jinya, lauyoyi da makamantansu su kasance da lasisin aiki mai inganci.
Kada mai nema ya taba aikata laifi ko kuma ya kasance da matsalar bashi.
Kada ya kasance da zanen tattoo a jikinsa.
Ya yi amfani da adireshin imel da lambar waya nasa masu aiki.
Ya bayyana dukkan takardun karatunsa da na kwarewa.
Mata masu juna biyu an shawarce su da kada su nemi aikin.
Ya mallaki cancantar karatu da ake bukata kamar SSCE, ND, NCE, HND, Digiri da sauran takardun da suka dace.
Direbobi da masu sana’o’i su kasance da Trade Test Certificate, lasisin tuki da sauran takardun da ake bukata.
Ya tanadi dukkan takardun da ake bukata kafin fara cike fom.
Takardun da za a gabatar sun hada da:
Takardar haihuwa ko shaidar rantsuwar shekaru.
Lambar NIN.
Takardun karatu.
Takardar NYSC ko ta kebewa (inda ya dace).
Lasisin aiki ga kwararru.
Trade Test Certificate ga masu sana’o’i.
Lasisin tuki (inda ya dace).
Takardar shaidar lafiya daga asibitin gwamnati.
Kwafin fom din da aka cike ta yanar gizo.
FRSC ta bukaci masu sha’awar aikin su gabatar da bukatunsu cikin wa’adin makonni hudu ta hanyar shafin daukar ma’aikata na hukuma, tare da kai rahoton duk wanda ya nemi kudi da sunan samar da aiki.
