Fitaccen mawakin Najeriya, , ya bayyana sabbin ra’ayoyinsa game da imaninsa da yadda yake kallon rayuwa da iyayensa.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar 22 ga watan Yuni, mawakin ya bayyana irin girman kauna da girmamawar da yake yi wa mahaifiyarsa da mahaifinsa.
9ice ya ce babu wani mutum ko wata halitta da yake bai wa matsayi mafi girma a rayuwarsa fiye da iyayensa, yana mai bayyana su a matsayin tushen daraja da albarka a gare shi.
Mawakin ya ce, “Ina son mahaifiyata, ina son mahaifina. Mahaifiyata ita ce Allahna, mahaifina shi ne Allahna.”
Ya bayyana cewa akidarsa da fahimtarsa game da ruhaniya sun sha bamban da yadda mutane da dama ke kallon lamarin, inda ya nuna cewa iyayensa su ne suka fi komai muhimmanci a rayuwarsa.
Kalaman mawakin sun jawo ce-ce-ku-ce da martani daga mabiyansa a kafafen sada zumunta, inda wasu suka bayyana cewa yana nufin girman matsayin iyaye ne a rayuwarsa, yayin da wasu kuma suka yi muhawara kan ma’anar kalaman nasa.
9ice na daga cikin fitattun mawakan Najeriya da suka yi fice musamman bayan fitowar wakarsa ta “Gongo Aso”, wadda ta sanya shi cikin manyan taurarin masana’antar waka a kasar.
