Fitaccen jarumin masana’antar fina-finan Nollywood, Charles Born, ya jawo hankalin mutane a kafafen sada zumunta bayan ya karrama mahaifiyarsa, Stella Born, a ranar bikin Uba (Father’s Day), yayin da ya yi waiwaye kan rayuwarsa ta yarinta da dangantakarsa da mahaifinsa.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Lahadi, jarumin ya bayyana mahaifiyarsa a matsayin wacce ta taka rawar uba a rayuwarsa.
Ya rubuta cewa: “Barka da Ranar Uba Dad. Ina son rubuta dogon sako, amma abin da zan fada kawai shi ne na gode. Ina matukar sonki.”
Sakon ya sake jawo hankalin jama’a zuwa wata hira da ya yi a baya a shirin Food Therapy wanda Chef Ify ke gabatarwa, inda ya bayyana irin wahalhalun da ya fuskanta a lokacin yarintarsa.
Charles Born ya ce bai samu kulawa, soyayya da goyon bayan da ya kamata yaro ya samu daga mahaifinsa ba, yana mai zargin cewa ya sha fuskantar cin zarafi ta fuskar magana da kuma duka.
A cewarsa, mahaifinsa kan yi masa kalamai masu raunana gwiwa kamar cewa ba zai taba zama komai a rayuwa ba.
Jarumin ya kuma bayyana cewa ya kan fuskanci azabtarwa ta jiki, lamarin da ya ce ya bar masa tabo na tunani da zuciya har zuwa yau.
Ya ce akwai wani lokaci da ya kai ga tunanin jefa kansa daga saman bene saboda irin azabar da yake ciki, amma wani makwabcinsu ne ya ceci rayuwarsa bayan ya shiga tsakani.
“Wani makwabcinmu ya ji hayaniya, ya zo ya karya kofar gilashi sannan ya dauke ni ya kai ni kasa,” in ji shi.
Duk da irin abubuwan da ya fuskanta, Charles Born ya tabbatar wa magoya bayansa cewa yana samun kulawar masana kan lafiyar kwakwalwa da tunani, kuma ya riga ya yafewa mahaifinsa.
Ya rubuta a sashen sharhi cewa: “Na gode da soyayyar da kuke nuna min. Ina cikin koshin lafiya kuma ina ci gaba da samun sauki. Na shafe shekaru ina zuwa wurin masu ba da shawara. Na yafewa mahaifina, ko da yake har yanzu ina kokarin mantawa da abubuwan da suka faru.”
Bayan wallafar sakon, mutane da dama sun yi ta yabawa mahaifiyarsa saboda yadda ta tsaya tsayin daka wajen rainonsa da kula da shi duk da kalubalen da ta fuskanta.
Wasu daga cikin mabiyansa sun bayyana cewa labarinsa ya nuna muhimmancin iyaye masu sadaukarwa, yayin da wasu suka yi addu’ar Allah ya saka wa mahaifiyarsa da alheri saboda irin gudunmawar da ta bayar wajen tarbiyyarsa.
Lamarin ya kuma sake bude tattaunawa kan muhimmancin lafiyar kwakwalwa, kula da yara da kuma rawar da iyaye ke takawa wajen gina rayuwar ‘ya’yansu.
