Fitaccen mawakin Najeriya Bella Shmurda ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta bayan wani bidiyon yadda ya yi wasa a wani taron dawowa gida (Homecoming Concert) da aka gudanar a Moshood Abiola Polytechnic (MAPOLY) ya karade intanet.
Bella Shmurda, wanda sunansa na asali Akinbiyi Abiola Ahmed, ya hau dandalin tare da mawaki Zlatan Ibile, inda suka nishadantar da dalibai da dimbin masoya.
Kafin ya fito fili, an ga jami’an tsaronsa biyu suna rakiyarsa cikin cunkoson jama’a, yayin da ya rufe fuskarsa da hular jaket dinsa kafin ya bayyana a dandalin.
Da zarar ya bayyana, daliban suka tarbe shi da sowa da tafi, yayin da jami’an tsaron suka ci gaba da kasancewa kusa da shi a tsawon lokacin wasan domin tabbatar da tsaronsa.
Bayan bidiyon ya yadu a kafafen sada zumunta, mutane sun fara bayyana ra’ayoyi mabambanta kan yadda mawakin ya gudanar da wasansa.
Wasu sun yi hasashen cewa wata kila yana cikin maye, tare da yabawa jami’an tsaron saboda yadda suka kasance kusa da shi a duk lokacin wasan. Wasu ma sun ce kamar Zlatan Ibile ya yi mamakin halayensa.
Sai dai wasu masoyansa sun ce babu wani abin mamaki a cikin wasan, suna bayyana cewa irin wannan kuzari da motsi na daga cikin salon Bella Shmurda a kan dandalin waka. Sun kuma kara da cewa kasancewar jami’an tsaro kusa da mawaka a irin wadannan manyan taruka abu ne na yau da kullum.
Sai dai, bidiyon da ya bazu bai tabbatar da dalilin halayen Bella Shmurda ba, kuma duk ra’ayoyin da ake yadawa a kafafen sada zumunta hasashe ne kawai.
