Jami’an tsaron Najeriya sun bayyana cewa karin jami’an tsaro da kuma katangar bincike da aka girke a sassan tsakiyar birnin Abuja wani bangare ne na matakan tabbatar da zaman lafiya da doka, ba wai saboda wata barazana ta musamman ba.
A yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da hukumomin tsaro da na leken asiri suka gudanar a ranar Alhamis, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, CSP Anietie Iniedu, ya tabbatar wa mazauna Abuja da baki cewa babu abin da ya kamata ya jawo fargaba.
Ya ce matakan tsaron sun biyo bayan karuwar zanga-zanga a tsakiyar birnin Abuja, inda hukumomin tsaro suka kara yawan jami’ai domin tabbatar da doka da oda tare da kare rayuka da dukiyoyi.
A cewarsa, Abuja a matsayinta na babban birnin Najeriya tana dauke da ofisoshin gwamnati, ofisoshin jakadanci da masu zuba jari daga kasashen waje, don haka wajibi ne a tabbatar da tsaro domin kara tabbatar da kwarin gwiwa ga mazauna birnin da baki.
Iniedu ya kuma bayyana cewa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta fadada tsarin aikinta daga dogaro da bayanan sirri kadai zuwa tsarin hadin gwiwa da al’umma wajen tattara bayanai da dakile barazanar tsaro.
Shi ma Kingsley Amako daga Hukumar Kula da Bayanan Sirrin Harkokin Kudi ta Najeriya (NFIU) ya ce hukumomin tsaro na ci gaba da inganta hanyoyin tattara bayanan sirri da sa ido kan hanyoyin samar da kudaden da ake amfani da su wajen tallafa wa ta’addanci.
Ya kara da cewa hukumomin tsaro na ci gaba da sabunta dabarunsu domin fuskantar sabbin salon da masu aikata laifuka ke amfani da su, duk da cewa ba za a iya bayyana wasu muhimman ayyukan tsaro ga jama’a ba saboda dalilan tsaro.
