Bankin Sterling Bank Limited ya bukaci Najeriya ta daina mayar da hankali kan fitar da albarkatun kasa a danyensu kawai, tare da karkata zuwa sarrafawa da kera kayayyaki masu karin daraja domin bunkasa kudaden shiga daga bangaren da ba na man fetur ba.
An bayyana wannan kira ne a yayin taron Excel in Non-Oil Export Forum karo na biyu da aka gudanar a Legas, mai taken “Reclaiming Sovereignty: Value Addition, Compliance, and the Future of Nigeria’s Non-Oil Export.”
Taron, wanda Sterling Bank ta shirya tare da hadin gwiwar Sunbeth Global Concepts, ya hada masu fitar da kayayyaki kasashen waje, hukumomin gwamnati da masana harkokin kudi domin tattauna matsalolin da ke hana bunkasar fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba.
Duk da cewa fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba ya kai matsayi mafi girma a tarihi a shekarar 2025, inda ya samar da kudaden da suka kai tiriliyan 6.1, man fetur har yanzu na samar da sama da kashi 80 cikin 100 na kudaden musayar kasashen waje da Najeriya ke samu.
Shugaban Sashen Bankin Kasuwanci na Sterling Bank, Akporee Idenedo, ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta sauya tsarin fitar da kayayyaki daga albarkatun kasa zuwa kayayyakin da aka sarrafa.
Ya bayyana cewa duk da kasancewar Najeriya ta hudu a duniya wajen samar da koko, har yanzu kasar ba ta amfana sosai daga kasuwar cakulan da aka sarrafa daga koko ba.
“Har yanzu muna fitar da damar ci gaba ne maimakon cikakken darajar kayayyakinmu. Dole ne mu daina fitar da danyen kaya kawai mu fara fitar da kayayyakin da aka kera kuma masu inganci,” in ji shi.
A nasa jawabin, Babban Masanin Tattalin Arziki kuma tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan tattalin arziki, Dakta Doyin Salami, ya bukaci mahalarta taron da su sake tunani kan yadda Najeriya za ta samu cikakken iko a harkokin kasuwanci ta duniya.
Ya ce Najeriya tana matsayi na 130 cikin kasashe 140 a ma’aunin Economic Complexity Index saboda ta fi mayar da hankali wajen fitar da albarkatun kasa maimakon kayayyakin da aka sarrafa.
Salami ya jaddada muhimmancin bin dokoki da ka’idojin kasuwancin duniya, yana mai cewa cika sharuddan inganci da kare muhalli ya zama wajibi ga duk mai son shiga kasuwannin duniya.
Ya kuma bayyana cewa bangaren ayyukan hada-hadar kudi, ciki har da biyan kudade tsakanin kasashe, ba da tallafin kasuwanci da bayanan tattalin arziki, na da damar zama babbar hanyar samun kudaden shiga ga Najeriya ba tare da dogaro da man fetur ba.
Sterling Bank ta bayyana cewa ta zuba jari sosai wajen horas da ‘yan kasuwa ta hanyar Non-Oil Export Academy da ta kafa tare da hadin gwiwar Enterprise Development Centre na Jami’ar Pan-Atlantic.
Idenedo ya ce tallafawa bangaren fitar da kayayyaki ba wai samar da jari kadai ba ne, har ma da bai wa ‘yan kasuwa ilimi da kwarewar da za su iya amfani da jarin yadda ya kamata a kasuwannin duniya.
Ya kara da cewa bankin na horas da ‘yan kasuwa a fannoni kamar kasuwancin kasa da kasa, takardun bashi, bin dokoki, sarrafa hadurra da samun damar shiga sabbin kasuwanni.
A cewarsa, hakan zai taimaka wajen sauya Najeriya daga fitar da albarkatun kasa zuwa kera kayayyaki masu karin daraja, wanda zai ba kasar damar cin gajiyar kasuwar mutane sama da biliyan 1.3 da yarjejeniyar cinikayyar Afirka (AfCFTA) ta samar.
Taron ya samu halartar jami’ai daga hukumomi da kungiyoyi daban-daban da suka hada da Hukumar NAFDAC, Hukumar SON, masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki a harkar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.
