Gwamnatin Tarayya ta bukaci masu kasuwancin man fetur da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren mai su rage farashin litar fetur da sauran kayayyakin man fetur domin ya yi daidai da faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur (Mai), Heineken Lokpobiri, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar tare da masu kasuwancin mai da hukumomin da ke kula da bangaren.
Lokpobiri ya ce farashin danyen man Brent ya sauka daga kusan dala 118 kan kowace ganga zuwa kasa da dala 70, don haka ya kamata ‘yan Najeriya su amfana da wannan sauyi ta hanyar rage farashin fetur.
Ya ce, “Farashin fetur ya kamata ya nuna halin da ake ciki a kasuwar duniya a yanzu.”
Ya kuma bayyana cewa tsarin cire tallafin mai ba yana nufin a rika samun ribar da ta wuce kima ba, yana mai cewa gwamnati ta fi son tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samar da mafita maimakon kakaba dokoki.
Bayan jawabansa na farko, mahalarta taron sun shiga ganawar sirri domin tattauna matsalolin da ke hana rage farashin fetur, ciki har da sarrafa ajiyar mai, sufuri, sa ido kan kasuwa da kuma dakile cin riba fiye da kima.
Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Tsakiya da Kasa (NMDPRA), Rabiu Umar, shi ma ya bukaci hadin kai tsakanin gwamnati da masu kasuwanci domin tabbatar da cewa raguwar farashin danyen mai ta bayyana a farashin fetur da masu amfani ke biya.
Ya ce manufar gwamnati ita ce samar da kasuwa mai gaskiya da adalci wadda za ta kare masu amfani da kuma ba ‘yan kasuwa damar gudanar da harkokinsu cikin riba.
Rabiu Umar ya kara da cewa irin wannan tattaunawa da aka yi a bangaren iskar gas makonni biyu da suka gabata ta taimaka wajen rage farashin gas na girki, yana mai fatan irin wannan hadin kai zai haifar da saukin farashin fetur.
Taron ya samu halartar wakilan Hukumar Kare Hakkin Mabukata (FCCPC), Matatar Dangote, MEMAN, DAPPMAN, IPMAN, NARTO, PETROAN da sauran kungiyoyin da ke bangaren mai.
