Wani sabon bincike ya bayyana cewa matsalolin tsaro da suka hada da ta’addanci, rikicin manoma da makiyaya da kuma sace-sacen mutane na kara jefa al’ummar Arewacin Najeriya cikin talauci tare da rage karfin iyalai na farfadowa daga matsin tattalin arziki.
Rahoton mai taken “Insecurity, Livelihoods and Welfare in Northern Nigeria” ya gano manyan matsalolin tsaro guda uku da suka fi addabar yankin Arewa. Wadannan sun hada da hare-haren Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas, rikicin manoma da makiyaya a Arewa ta Tsakiya da kuma ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma.
An bayyana sakamakon binciken ne a wani taron yanar gizo da aka gudanar a Abuja, wanda cibiyar Chronic Poverty Advisory Network (CPAN) ta kasar Birtaniya, Development Research and Projects Centre (dRPC) da kuma shirin Strengthening Peace and Resilience in Nigeria (SPRiNG) suka shirya.
Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro, ya halarci taron inda ya yi tsokaci kan muhimmancin sakamakon binciken ga manufofin gwamnati na yaki da talauci.
Yayin gabatar da rahoton, Mataimakiyar Daraktan CPAN, Dakta Vidya Diwakar, ta bayyana cewa binciken ya yi amfani da bayanai daga binciken rayuwar al’umma na Najeriya na shekarar 2022/2023, binciken lafiya da al’umma na 2024 da kuma bayanan rikice-rikice daga shekarar 2010 zuwa 2025.
Rahoton ya nuna cewa iyalan da hare-haren Boko Haram da ISWAP suka shafa a Arewa maso Gabas sun samu raguwar kashe-kashen rayuwa da kashi tsakanin takwas zuwa 14 cikin dari idan aka kwatanta da sauran gidaje.
Haka kuma, bashin da ya samo asali daga rikice-rikice tun daga shekarar 2009 ya kara janyo asarar kudaden rayuwa da kashi tsakanin takwas zuwa 13 cikin dari.
Binciken ya kuma gano cewa rikicin manoma da makiyaya a Arewa ta Tsakiya shi ne ya fi haddasa mummunan tasiri ga iyalan da ke kusa da layin talauci, inda aka samu raguwar kudaden rayuwa da kashi 14 cikin dari.
A Arewa maso Yamma kuwa, ayyukan ‘yan bindiga da garkuwa da mutane sun haddasa asarar kudaden rayuwa da ke tsakanin kashi hudu zuwa 11 cikin dari, musamman ga gidajen da ke fama da matsakaicin talauci.
Sai dai rahoton ya bayyana cewa hada hanyoyin samun kudin shiga daban-daban ita ce hanya mafi tasiri wajen taimakawa iyalai su jure kalubalen talauci da rikice-rikice.
Binciken ya nuna cewa hada noma, sana’o’in hannu da sauran harkokin kasuwanci na taimakawa wajen kare iyalai daga fadawa cikin matsanancin talauci.
Duk da haka, rahoton ya nuna cewa kashi 13 cikin dari kacal na shugabannin gidaje a Arewacin Najeriya ne ke da hanyoyin samun kudin shiga fiye da daya.
Masana da suka yi sharhi kan binciken sun jaddada muhimmancin hada kokarin samar da zaman lafiya da shirye-shiryen farfado da hanyoyin samun abin rayuwa domin rage talauci da karfafa zaman lafiya mai dorewa.
Sun kuma bukaci a kara horas da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma domin su taka muhimmiyar rawa wajen sasanta rikice-rikice da inganta zaman lafiya a yankunansu.
A karshen taron, gwamnatin tarayya ta yi alkawarin ci gaba da hada kai da masu ruwa da tsaki wajen aiwatar da manufofin rage talauci tare da amfani da bincike da hujjoji wajen tsara shirye-shiryen da za su amfani mata da matasa, wadanda galibi ke fuskantar kalubalen samun tallafi.
