Wani dan kasuwar Najeriya da ke gudanar da harkokinsa a Afirka Ta Kudu ya yi fatali da matsin lambar da wasu masu zanga-zanga ke yi na rufe shagonsa, yana mai cewa matakin zai jefa ma’aikatan Afirka Ta Kudu sama da 30 cikin matsalar rashin aiki.
A cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, an ga dan kasuwar yana tattaunawa da wasu masu zanga-zanga da ke neman a rufe dukkan shagunan da baki ke gudanarwa a kasar.
Sai dai ya bayyana cewa yana da dukkan takardun da suka dace, yana biyan haraji tsawon shekaru 13 da suka gabata, kuma kasuwancinsa na samar da ayyukan yi ga dimbin ‘yan Afirka Ta Kudu.
“Lokacin da ‘yan China ke gudanar da wannan shago, mutum daya ko biyu ne kawai ke aiki a ciki. Amma tun lokacin da na karbi kasuwancin, na samar da ayyukan yi ga tsakanin mutum 20 zuwa sama da 30 ‘yan Afirka Ta Kudu,” in ji shi.
Masu zanga-zangar dai sun dage cewa ba sa son baki su ci gaba da gudanar da kasuwanci a yankin, suna masu bukatar ya rufe shagonsa nan take.
Dan kasuwar ya ce zai amince ya rufe kasuwancin ne kawai idan gwamnatin Afirka Ta Kudu ta bayar da umarni a hukumance, yana mai jaddada cewa ba dan kasa ba ne mai zama ba bisa ka’ida ba.
“Na yi kasuwanci tare da biyan haraji tsawon shekaru 13. Ba na zaune a kasar ba bisa ka’ida ba. Idan gwamnati ta ce in rufe shagona in tafi, zan yi hakan,” ya bayyana.
Ya kara da cewa babban abin da ya fi damunsa shi ne makomar ma’aikatansa, yana mai cewa ba zai so ya bar su cikin mawuyacin hali ba.
“Ma’aikatana sama da 30 ‘yan Afirka Ta Kudu ne. Idan aka rufe wannan shago, za su rasa ayyukansu. Ina son in tabbatar suna cikin aminci kafin na tafi.”
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da wasu kungiyoyin adawa da bakin haure a Afirka Ta Kudu ke kara matsa lamba ga baki marasa takardu su fice daga kasar.
A halin yanzu, gwamnatin Afirka Ta Kudu ta fara mayar da ‘yan Najeriya 586 da aka ce suna zaune a kasar ba bisa ka’ida ba, inda rukuni na farko ya isa Lagos a makon da ya gabata.
Rahotanni sun kuma nuna cewa gwamnatin Afirka Ta Kudu ta fara nuna damuwa kan yadda zarge-zargen kyamar baki ke shafar harkokin kasuwanci da ayyukan ‘yan kasar a wasu kasashen duniya.
