Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya bayyana cewa wasu kungiyoyin masu aikata laifuka na amfani da sunan kwamitin gwamnatin tarayya wajen sace bututun mai a sassan kasar nan.
Kamfanin ya ce an samu rahotannin lalata bututun mai guda 24 tun daga shekarar 2025, inda aka sace kusan kilomita tara na bututun mai. NNPC ta kara da cewa jami’an tsaro sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a ayyukan satar bututun mai a yankin Kwali da ke Abuja.
Kamfanin ya jaddada cewa zai ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro domin kamo masu hannu da shuni da ke daukar nauyin wannan ta’asa tare da kare muhimman kadarorin makamashi na kasa.
