Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Alliance (AA) a zaben shekarar 2027, Adekunle Omo-Aje, ya bukaci gwamnatoci da hukumomin tsaro su kara kaimi wajen kawo karshen matsalar ‘yan bindiga, satar mutane da ta’addanci a fadin Najeriya.
Omo-Aje ya bayyana hakan ne a sakonsa na bikin Ranar Dimokuradiyya, inda ya ce ribar dimokuradiyya ba za ta cika ba matukar jama’a ba su samu tsaro da walwala a rayuwarsu ta yau da kullum ba.
Ya nuna cewa duk da shekaru 26 da Najeriya ta yi tana tafiyar da mulkin dimokuradiyya ba tare da katsewa ba, har yanzu al’ummomi da dama musamman a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya na fama da matsalar rashin tsaro, talauci da karancin ababen more rayuwa.
A cewarsa, dimokuradiyya ba wai zabe da mukaman siyasa kadai ba ne, illa tana nufin inganta rayuwar talakawa da tabbatar da jin dadinsu.
“Dole ne ‘yan Najeriya su ga tasirin dimokuradiyya a rayuwarsu. Tsaro, ayyukan yi da ababen more rayuwa su ne ginshikan ci gaba,” in ji shi.
Omo-Aje ya bukaci gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi su mayar da hankali wajen samar da tituna masu kyau, ingantacciyar wutar lantarki, ruwa da sauran muhimman ayyukan raya kasa.
Dangane da tattalin arziki, ya bukaci gwamnati ta dauki matakan samar da ayyukan yi, tallafawa kanana da matsakaitan sana’o’i tare da rage tsadar rayuwa da ke addabar ‘yan kasa.
Ya kuma jaddada cewa tsaro na daga cikin manyan nauyin da ya rataya a wuyan kowace gwamnati ta dimokuradiyya, yana mai kira ga shugabanni da jami’an tsaro su dauki matakan gaggawa domin murkushe ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
A cewarsa, kara zuba jari a tattara bayanan sirri, inganta tsarin tsaron al’umma da samar wa jami’an tsaro kayan aiki na zamani zai taimaka wajen magance matsalar tsaro.
Ya gargadi cewa fannonin noma, ilimi da lafiya ba za su samu cikakken ci gaba ba matukar rashin tsaro ya ci gaba da addabar al’umma.
A karshe, Omo-Aje ya yabawa ‘yan Najeriya bisa jajircewarsu wajen kare dimokuradiyya duk da kalubalen tattalin arziki da tsaro, tare da kira ga jama’a su ci gaba da rike shugabanni da alhakin ayyukansu domin tabbatar da shugabanci nagari.
