Kamfanin binciken sararin samaniya na Elon Musk, SpaceX, ya shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Wall Street a karon farko bayan kammala sayar da hannayen jari (IPO) mafi girma a tarihi, inda ya tara sama da dala biliyan 75.
Wannan gagarumin nasara ta sa ana hasashen Musk zai iya zama mutum na farko a duniya da dukiyarsa za ta kai tiriliyan guda na dala.
Yayin bikin kaddamar da IPO din a Starbase da ke jihar Texas, Musk ya bayyana cewa babban burin SpaceX shi ne kai mutane zuwa Wata, duniyar Mars da ma sauran duniyoyi da ke sararin samaniya.
“SpaceX na son kai ku zuwa Wata, zuwa Mars, har ma fiye da haka. Ina da yakinin cewa za mu cimma hakan tare da kwararrun ma’aikatanmu,” in ji Musk.
Kamfanin ya fitar da sama da hannayen jari miliyan 555 a farashin dala 135 kowanne, lamarin da ya daga darajar SpaceX zuwa kusan dala tiriliyan 1.8, wanda ya sanya shi cikin manyan kamfanoni goma mafi girma a Wall Street.
SpaceX, wanda Musk ya kafa a shekarar 2002, ya bunkasa daga kamfanin harba rokoki zuwa babban kamfanin sadarwar tauraron dan adam ta Starlink, sannan ya hade da kamfanin fasahar basirar wucin gadi na xAI, wanda ke gudanar da manhajar Grok da kuma dandalin X.
Duk da cewa kudaden shigar kamfanin sun kai dala biliyan 18.7 a shekarar 2025, SpaceX ya yi asarar kusan dala biliyan 4.9 sakamakon manyan kudaden da yake kashewa wajen bunkasa fasahar AI da sauran manyan ayyuka.
Masu zuba jari da dama sun nuna matukar sha’awa ga IPO din, inda rahotanni suka nuna cewa bukatar sayen hannayen jarin ta zarce adadin da aka fitar fiye da sau hudu.
Sai dai wasu masana na nuna damuwa kan yadda darajar kamfanin ke dogaro da manyan alkawuran Musk na kai mutane zuwa Mars, gina cibiyoyin bayanai a sararin samaniya da kuma fadada ayyukan Starlink da xAI.
Idan SpaceX ta samu nasara a kasuwar hannayen jari kamar yadda ake hasashe, hakan zai kara habaka dukiyar Elon Musk tare da kafa sabon tarihi a duniya.
