Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) ta shawarci iyaye da masu kula da masu bautar kasa da su rika ba su isassun kudin sufuri yayin tafiya zuwa sansanonin horo a fadin kasar.
Babban Daraktan NYSC, Olakunle Nafiu, ne ya bayar da wannan shawara a ranar Laraba yayin wani taro da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya shirya a Abuja.
Ya ce ya fi dacewa iyaye su kara wa ‘ya’yansu kudin hanya domin su iya tsayawa hutawa cikin aminci idan tafiya ta yi nisa ko dare ya yi, maimakon su ci gaba da tafiya cikin hadari.
Nafiu ya bayyana cewa wasu masu bautar kasa kan yi amfani da kudin hanyarsu gaba daya a tafiya daya, wanda ke sa su kin tsayawa ko da yanayin tafiya ya zama mai hadari.
Ya gargadi masu bautar kasa da su guji tafiya da daddare, yana mai cewa hakan na iya jefa su cikin hadarin satar mutane da sauran matsalolin tsaro.
Ya kuma shawarce su da su fara shirin tafiya da wuri bayan samun lambobin kiransu na NYSC domin kauce wa gaggawa da rashin tsari.
“Bayan karfe shida na yamma kada su yi tafiya. Idan dare ya yi, su tsaya su kwana su ci gaba washegari,” in ji shi.
Daraktan ya kara da cewa NYSC ta kara hadin gwiwa da jami’an tsaro kamar ‘yan sanda da sojoji domin tabbatar da tsaron masu bautar kasa a hanyoyin tafiya.
Ya ce ana kuma rakiyar wasu masu bautar kasa a wuraren da ake ganin suna da hadari domin tabbatar da sun isa sansanonin lafiya.
Nafiu ya kuma gargadi mutane da su guji bayar da kudi ga masu ikirarin sauya wurin tura masu bautar kasa, yana mai cewa tsarin tura su na gudana ne ta kwamfuta kawai.
Ya bayyana cewa matan aure da masu matsalolin lafiya ne kawai ake yi wa sauyi na musamman zuwa wuraren da ke kusa da iyalansu ko cibiyoyin lafiya.
