Tsohon gwamnan jihar Gombe kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa, Ibrahim Dankwambo, ya samu sahalewar jam’iyyar PDP domin sake tsayawa takarar kujerar Sanata a zaben 2027.
Dankwambo na daga cikin ‘yan takarar da kwamitin tantance ‘yan takarar PDP ya amince da su domin shiga zaben fidda gwani na majalisar dokoki ta kasa a jihar Gombe.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun zazzafar siyasa a yankin Gombe ta Arewa, bayan rahotannin cewa gwamnan jihar, Muhammadu Yahaya, shi ma ya samu sahalewar APC domin neman kujerar Sanata bayan karewar wa’adinsa na mulki.
PDP ta bayyana hakan ne cikin wata wasika da sakatariyar jam’iyyar a jihar Gombe ta aikawa shugaban jam’iyyar na kasa ta hannun sakataren shirye-shirye na kasa, inda aka bayyana sunayen ‘yan takarar Sanata da na majalisar wakilai da aka tantance.
Shugaban kwamitin tantancewar, Mohammed Dan’azumi Adamu, da sakataren kwamitin, Musa Abubakar, tare da sakataren PDP na jihar, Alhaji Adamu Abubakar ne suka sanya hannu a takardar.
A cewar takardar, Anthony Siyako Yaro ya samu sahalewa domin takarar Sanatan Gombe ta Kudu, yayin da Aliyu Hammadu ya samu sahalewa domin Gombe ta Tsakiya.
Haka kuma, jam’iyyar ta tantance Gidado Alhaji Lawanti domin mazabar Akko, Mohammed Lamido domin Dukku/Nafada, da Dr. Obed Paul Shehu domin Kaltungo/Shongom.
Sauran sun hada da Dr. Nasir Ibrahim domin Gombe/Kwami/Funakaye, Shu’aibu Umar Galadima domin Yamaltu/Deba, da Rambi Ibrahim Ayala domin Balanga/Billiri.
