Kungiyar ‘yan fansho ta Najeriya reshen Kudu maso Gabas ta yabawa gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo, bisa biyan bashin gratuity na shekaru hudu da aka dade ana bin tsofaffin ma’aikata a jihar.
Shugaban kungiyar a yankin Kudu maso Gabas, Anthony Ugozor, ya bayyana cewa bashin wanda ya kai naira biliyan 22 ya shafi kudaden gratuity daga shekarar 2017 zuwa 2020, wadanda gwamnatin da ta gabata ta bari.
Ugozor ya bayyana hakan yayin taron kungiyar da aka gudanar a Awka, inda ya bukaci sauran gwamnoni a yankin da su yi koyi da Soludo wajen kula da walwalar ‘yan fansho da tabbatar da biyan hakkokinsu cikin lokaci.
A cewarsa, gwamnatin Soludo tana biyan tsofaffin ma’aikata kudaden fansho ba tare da jinkiri ba, tare da biyan gratuity ga wadanda suka yi ritaya.
Ya kuma bukaci gwamnoni su aiwatar da sabon tsarin mafi karancin fansho na naira 32,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi domin rage wahalar rayuwa da ‘yan fansho ke fuskanta.
Ugozor ya koka kan yadda wasu ‘yan fansho masu matakin aiki iri daya ke samun bambancin albashi duk da cewa sun yi aiki a mataki guda.
Haka kuma, ya tunatar da gwamnatin Anambra kan kudin naira miliyan 490.18 da ake bin wasu tsofaffin malaman firamare na shekarun 2002 da 2003, yana mai cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun rasu kafin samun hakkokinsu.
A nata bangaren, Shugabar Ma’aikatan gwamnatin jihar Anambra, Ngozi Iwuno, ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kula da walwalar ‘yan fansho tare da girmama gudummawar da suka bayar wajen ci gaban kasa.