Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama wani mutum mai shekaru 30 mai suna Okechukwu Chinweko, wanda aka fi sani da “Bullet”, bisa zarginsa da hannu a garkuwa da mutane, fyade da kuma mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.
Rahotanni sun ce an gano tambarin tattoo da aka rubuta “Bullet” a hannunsa, wanda ya taimaka wajen danganta shi da wani lamari da ya faru ranar 2 ga Mayu, 2026, inda ake zarginsa da sace wata mata tare da yi mata fyade kafin jami’an ‘yan sanda su ceto ta.
An bayyana cewa wanda ake zargin ya tsere daga wurin bayan ya jikkata matar da raunuka daban-daban.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Ikenga ya ce jami’an rundunar Rapid Response Squad da ke Awkuzu sun kama wanda ake zargin ne a maboyarsa da ke yankin Umudike a Awka, bayan samun sahihan bayanan sirri da gudanar da bincike.
Ya kara da cewa yayin samamen, jami’an sun kwato wata bindigar Beretta da aka kera a gida tare da harsasai guda takwas masu girman 9mm.
A cewar sanarwar, binciken farko ya nuna cewa an tabbatar da hannun wanda ake zargin a lamarin sace da fyaden matar, wadda aka same ta da raunuka a jikinta bayan jami’an tsaro sun ceto ta.
Rundunar ‘yan sandan Anambra ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a tare da gurfanar da masu aikata laifuka a gaban kuliya komai tsawon lokaci.
