Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta bayyana damuwa kan yadda ake ƙara amfani da bara da kuma mutane marasa galihu a cikin hanyoyin aikata laifuka, musamman wajen safarar miyagun kwayoyi a birnin Abuja.
Sakataren Cibiyar Kula da Tsaro da Gudanarwa ta FCT, Peter Olumuji, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin ci gaba da aikin sintiri mai taken Operation Sweep, inda ya ce bayanan leƙen asiri sun nuna cewa wasu masu laifi na amfani da masu rauni a cikin al’umma domin jigilar miyagun kwayoyi.
Olumuji ya ce ana amfani da bara da kuma masu nakasa a matsayin masu kai kaya, musamman da daddare, domin guje wa shakku daga jami’an tsaro.
“Abin takaici shi ne, duk da yadda suke cikin mawuyacin hali, an mayar da su kayan aiki a hannun masu aikata laifi,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Daga bayanan da muka tattara, ana amfani da su wajen kai miyagun kwayoyi musamman da daddare.”
Olumuji ya ce wannan dabara na taimaka wa masu laifi wajen kaucewa kamawa, saboda ba a saba zargin masu nakasa da irin wannan aiki ba.
Ya kuma bayyana cewa a wasu lokuta jami’an sintiri na fuskantar turjiya daga wadanda ake zargi, inda wasu ke amfani da sandunan tafiya da sauran kayan taimako wajen kai hari ga jami’an.
Hukumar FCTA ta ce aikin na cikin shirin tsaftace birnin daga bara da rashin tsaro, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsari a manyan wuraren Abuja.
Shugabar aikin sintiri, Ulkacha Adebayo, ta ce an kama mutane 54 a aikin ranar Litinin, ciki har da manya 45 da yara tara.
Ta ce a cikin watanni uku da suka gabata an tattara sama da mutane 835, wanda idan aka hada da na yanzu ya kai 889.
Adebayo ta ce wadanda aka kama ana tantance su sannan a tura su cibiyoyin gyaran hali domin horas da su sana’o’i da kuma tallafin jin kai.
Ta bayyana cewa aikin zai ci gaba a manyan wurare kamar Maitama, Asokoro, Garki, Wuse da Gwarinpa, bisa umarnin Ministan FCT, Nyesom Wike.
